21 Oktoba 2020 - 16:02
Ana Samun Tashe-tashen Hankula A Birkin Lagos Da Ke Nigeria

Rahotannin da suke fitowa daga birnin na Ikko suna nuni da cewa wasu samari da suke cikin fushi sun kai hare-hare a wurare daban-daban da suka hada da tashar talabiji ta TVC wacce mallakin Sanata Ahmad Tinubu ce.

ABNA24 : A jiya Talata ne dai aka zargin sojojin kasar da bude wuta akan masu Zanga-zangar da su ka taru a gabar ruwa na Lekki, a ci gaba da kiraye-kirayen da ake yi na kawo karshen halin ketar ‘yan sandan kasar.

A gefe daya gwamnan jahar ta Lagos ya gabatar da jawabi inda a ciki ya nemi gafafar abinda ya faru, a jiya sannan kuma ya sanar da dakatar da duk wasu ayyun in ba muhimmai ba ne a fadin jihar.

342/