19 Oktoba 2020 - 12:48
An Kawo Karshen Takunkumin Hana Iran Saye Da Sayar Da Makamai

A safiyar yau Lahadi ne takunkumin da Majalisar Dinkin Duniya ta sanya wa Jamhuriyar ta Iran na saye da sayar da makamai ya kawo karshe, don haka daga yanzu Iran tana da hakkin saye ko kuma sayar da makamai a kasuwar duniya.

ABNA24 : A bisa yarjejeniyar da aka cimma da Iran cikin yarjejeniyar nukiliya a shekara ta 2015, an tsayar cewa za a kawo karshen wannan takunkumin na MDD a kan kasar wanda ya zo cikin kudurin kwamitin tsaro mai lamba 2231 cewa daga ranar 18 ga watan Oktoban 2020 ne za a dage wannan takunkumin.

Tun da safiyar yau din ne dai Ma’aikatar harkokin wajen ta Iran, cikin wata sanarwa da ta fitar ta bayyana cewar: Daga yau Lahadi ne za a kawar da duk wani tarnaki akan zirga-zirgar makamai daga jamhuriyar Musulunci da kuma zuwa cikinta. Haka nan kuma kai da komowar kudade da suke da alaka da hakan.

Tun dai bayan da aka sanya wa Iran wancan takunkumi na sayen makaman ne Ma’aikatar tsaron kasar da sauran cibiyoyin tsaro suka dukufa wajen kera nau’oi daban-daban na makamai don tabbatar da tsaron kasar lamarin da ana iya cewa ya zuwa yanzu Iran din ta samu nasarar kera makamai daban-daban na zamani masu tasirin gaske cikin tsaron kasar.

Kasar Amurka dai ta yi ta kai gwauro ta kai mari wajen ganin an tsawaita takunumin hana Iran mallakar makaman ko kuma sayar da su, to amma ta sha kunya a Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, inda membobin kwamitin da suaran kasashen duniya suka yi watsi da wannan bukata nata.

342/