ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran Fars na Iran ya bayyana cewar Janar Salami ya bayyana hakan ne a yau din a wani taro da aka gudanar da dubi cikin hanyoyin da za a bi wajen aiwatar da umurnin da Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Khamenei ya bayar ga sojojin Iran na shigowa cikin fadar da ake yi da cutar Coronavirus din inda ya ce dakarun IRGC din a shirye suke su ci gaba da gabatar da dukkanin abin da suke da shi na kwarewa da kayan aiki wajen aiwatar da umurnin Jagoran.
Har ila yau babban kwamandan dakarun na IRGC ya ce baya ga bangaren ba da magani, har ila yau dakarun IRGC din sun kaddamar da wani shiri na taimakon mutanen da cutar da Korona ta tagayyara ta hanyar ba su agaji na abubuwan gudanar da rayuwa.
Tun dai bayan bullar cutar Koronan a Iran, dakarun IRGC sun kaddamar da gagarumin aikin fada da ita ta hanyar kirkiro asibitin tafi da gidanka da sauran duk dai da nufi kula da wadanda cutar da kama su da kuma ba su magani.
342/