9 Oktoba 2020 - 14:22
Iran Da Venezuela Za Su Fadada Dangantakar ake Tskaninsu A Bangaren Yawon Shakatawa

Ministan al’adu da kuma yawon shakatawa na kasar Iran ta kuma ministan al’adu na kasar Venezuela sun tabbatar da cewa kasashen biyu zasu fadada dangantakar yawon shakatawa tsakanin kasashen biyu.

ABNA24 : Majiyar muryar JMI ya nakalto Ali Asgar Munison da kuma Felix Plasencia suna fadar haka a jiya Laraba a wani taron yan jarida da suka kira a nan Tehran.

Munison ya ce ma’aikatarsa ta taimakawa ‘yan kasuwa masu zaman kansu a kasar Iran gina Otel Otel har guda 498. Sannan a shekara ta 2019 da ta gabata kasar Iran ce kasa ta biyu a duniya wajen saurin fadada bangaren yawon shakatawa a duniya.

A nashi bangaren Felix Plasencia ya ce Tehran da Caracas zasu yi musayar kwarewa a bangaren yawon shakatawa a tsakanin don samar da ci gaba a wannan fagen a kasashen biyu.

342/