9 Oktoba 2020 - 14:11
Mali : An Sallami Jagoran ‘Yan Adawa Na Mali, da ‘yar Agajin nan ta Faransa

Rahotanni daga Mali na cewa an saki wata Bafaranshiya ma’aikaciyar agaji, Sophie Petronin mai shekaru 75 da aka yi garkuwa da ita tun shekarar 2016 tare da shugaban 'yan adawan kasar Soumaila Cisse mai shekaru 70

ABNA24 : Ofishin shugaban kasar Mali ya fara sanar da sakin Petronin da Cisse da ake zargin kungiyar Al Qaeda da sace su kafin daga bisani suka sauka filin jirgin saman Bamako.

Wannan na zuwa ne bayan sakin mutane akalla 100 daga cikin wadanda ake zargi ko kuma aka yankewa hukuncin aikata laifuffukan masu nasaba da ta’addanci.

Ita dai gwamnatin ba ta yi bayani kan yadda aka saki wadannan mutane biyu ba.

Ita dai Petronin an sace ta ne ranar 24 ga watan Disamban shekarar 2016 a Gao da ke arewacin kasar, kuma ita ce 'yar Faransa ta karshe da ake garkuwa da ita a duniya.

Shi kuwa Cisse, wanda sau uku yana takarar shugaban kasa, an sace shi ne ranar 25 ga watan Maris lokacin da yake yakin neman zabe a Niafounke.

342/