ABNA24 : Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Iran ne, Saeed Khatibzadeh, ya sanar da hakan.
Iran ta ce tana sanya ido sosai kan rikicin dake faruwa a kusa da iyakokinta na arewa maso yamma, kuma tana kan tattaunawa da bangarorin biyu.
Dama tun farkon rikicin, Iran, ta bayyana cewa, yaki ba shi ne mafita ba game da dadaden rikicin dake tsakanin kasashen biyu kan yankin Karabakh.
Iran, ta ce ta hanyar mutumta hurimin kasar Azerbaijan da kuma bukatar janje dakaru daga yankunan da aka mamaye ta wannan ne za’a iya shawo kan rikicin.
Kan hakan kuma Iran, ta shirya wani tsari wanda bangarorin biyu dake rikici da kasashen yankin zasu tattaunawa a kai.
Har Illah yau dai Iran, ta sake bukatar kasashen biyu dasu tsagaita wuta a tsakaninsu, tare da gargadinsu akan ba zata lamunci duk wani irin kuskure ba na yin kuste a cikin kasarta ba.
342/