4 Oktoba 2020 - 11:49
Annobar Korona Ta Jawo Rufewar Majalisar Dattawan Amurka

Shugaban majalisar dattawan Amurka kuma shugaban jam’iyyar Republican mai rinjaye a majalisar Mitch McConnell ya bada sanarwan rufe majalisar na makonni biyu saboda cutar korona.

ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Mitch McConnell yana fadar cewa an rufe majalisar ne saboda kowa ya je ya gwada cutar Korona daga jiya Asabar.

Kafin haka dai shugaban kasar ta Amurka Donal Trump da kuma matarsa Melenia duk sun kamu da cutar, sannan a halin yanzu yana jinya a wani asbiti a birnin na washongton.

Trump dan shekara 74 a duniya kuma wanda yake da jiki fiye da kima, zai sha wahala kafin ya warke.

Banda shugaban dai wasu da dama daga cikin mukarrabansa wadanda suka hada da Mike Pompeo sakataren harkokin wajen kasar da kuma matarsa duk sun kamu da cutar.

A halin yanzu dai Amurka ce a gaba da yawan wadanda suka kamu da cutar da kuma yawan wadanda suka rasa rayukansu sanadiyyar ta a duniya.

342/