ABNA24 : Har ila yau, ministocin kasashen biyu sun yi kira ga dukkanin bangarorin Azerbaijan da Aremnia da su kaucewa yin maganganu da tsokana da za su kara ruruta wutar yaki.
Bugu da kari, kasashen na Iran da Rasha, sun bayyana cewa kasashen yanki da kuma makwabta za su iya taka rawa wajen samar da yanayin komawa kan teburin tattaunawa tsakanin Azerbaijan da kuma Armenia.
Kasashen Armenia da Azerbaijan sun koma yaki akan iyakokinsu a ranar Lahadi 27 ga watan Satumba, suna masu zargin juna da fara tsokana.
342/