1 Oktoba 2020 - 11:39
Rauhani: Iran A Shirye Take Ta Shiga Tsakani Domin Warware Fada Tsakanin Armeniya Da Azerbaijan

Shugaban kasar na Iran Dr. Hassan Rauhani ya bayyana hakan ne a lokacin da yake tsokaci a kan yakin da ake yi tsakanin kasashen Azerbaijan da Armenia akan yanklin Kharabagh.

ABNA24 : Shugaba Dr. Hassan Rauhani ya kuma tattauna ta wayar tarho da Fira ministan kasar Armenia Nikol Pashinyan, inda ya jaddada muhimmancin zaman lafiya da tsaro a yankin.

Dr. Hassan Rauhani ya kuma kara da cewa; A halin yanzu wannan yankin baya da bukatuwa da Karin rikice-rikice bayan wadanda yake fama da su.

Wani sashe na maganar shugaban kasar ta Iran, ya kunshi yin kira da warware sabanin da yake tsakanin kasar ta Armenia da Azerbaijan ta hanyar dogaro da dokokin kasa da kasa.

342/