ABNA24 : Jaridar Al-Ahad ta kasar Lebanon ta nakalto jam’iyyun siyasar da kuma fitattun ‘yan kasar ta Lebanon suna fadar haka a yau Talata bayan sun kammala tattauna batun a ofishin kungiyar Amal na yankin Biqa a kudancin kasar ta Lebanon.
A cikin wani rahoton da suka fitar jam’iyyun siyasar sun zargi shugaban kasar na Faransa da kokarin maido da halayen gwamnatin kasar Faransa na mulkin mallaka a kan kasar Lebanon sannan sun kara jaddada cewa a halin yanzu kasar Lebanon ‘yantacciyar kasar ce wacce babu wata kasa a duniya da take da hurumin tilasta mata aiwatar da abubuwan da take so a kasar.
Bayan fashewar da ta auku a tashar jiragen ruwa na birnin Beirut babban birnin kasar Lebanon a ranar 4 ga watan Augustan da ya gabata, shuwagabaninin manya-manyan klasashen duniya wadanda suka hada da Amurka da kuma Farasansa sun zo kasar ta Lebanon wasu kuma sun bayyana maitansu na kokarin nuna iko a yadda kasar take tabiyar da harkokin siyasar kasar.
342/