ABNA24 : A jiya ne shugaban kasar Faure Gnassingbé, ya nada Madame Victoire Sidémèho Tomegah, a matsayin fira ministar kasar.
Ita ce kuma mace ta farko da zata riki wannan mukami a tarihin kasar tun bayan data samu ‘yancin kanta.
Dama Kafin rike wannan mukamin ita ce darektar fadar shugaban kasar, kana kuma tana rike da mukamin ministar kula da ayyukan ci gaba, wanda hade yake da ayyukan hannu da samar da ayyukan yi ga matasa.
Jan aikin dake gaban sabuwar fira ministar a wannan lokaci da ake fama da annobar korona, yin aiki tukuru domin samar da ci gaba mai daurewa, daya daga cikin alkawuran da shugaban kasar Faure Gnassingbé, ya sanya a gaba a wannan wa’adin mulkinsa na hudu.
A ranar Juma’ar data gabata ce fadar shugaban kasar Togo ta sanar da murabus din Fira ministan kasar, Komi Sélom Klassou, da shi da illahirin mambobin gwamnatinsa.
Bayanai daga kasar sun ce tun ba yau ne ba ake tsammanin nada sabuwar gwamnatin a kasar ta Togo, bayan da shugaba Gnassingbé, ya sake lashe zaben shugabancin kasar, saidai hakan bai yi wu ba saboda halin da aka shiga na annobar korona.
342/