ABNA24 : Majiyar muryar Jumhuriyar Musulunci ta Iran (JMI) ta nakalto hukumar ta na fadar haka ne a cikin shafinta na Twitter a jiya Asabar, wacce ta yi dai-dai da ranar 26 ga watan Satumba, ranar da MDD ta ware don raya fasahar nukliya ta zaman lafiya a duniya.
Ma’aikatar ta kara da cewa a rana irin ta yau ne yakamata a sanar wa duniya kan cewa amfani da fasahar nukliya ta zaman lafiya da ci gaba, hakki ne na ko wace kasa a duniya, sannan a nunawa kasashe masu girman kai a duniya kan cewa ba hakkinsu ba ne su takaita wannan fasahar a tsakaninsu ba.
Kafin haka dai ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta bayyana cewa HKI ce babbar barazana a yankin Asia ta kudu don makaman nukliyan da ta tara a yankin.
342/