ABNA24 : Tashar talabijin ta Presstv ta nakalto Janar Salami yana fada a bikin kaddamar da aikin kan cewa Kam fanin ayyulkan gine-gine na Khatamul Ambiya tare da wasu na cikin gida ne zasu gudanar da aikin gina matatan man a wani wuri kilomita 18 daga birnin Bandar Abbas a bakin tekun Farisa.
Salami ya kammala da cewa dakarun juyin juya halin musulunci zasu ci gaba da ayyukan kai kasar Iran gaba duk tare da munanan takunkuman tattalin arziki na kasar Amurka da kasar take fama da su.
342/