16 Satumba 2020 - 15:28
Palasdinawa Sun Raya Ranar “Kasa” Ta Tunawa Da Kwace Palasdinu

A yau Talata ne dai dubban palasdinawa suka gudanar da jerin gwano domin raya ranar kasa wacce ta zo daidai da kulla yarjejeniya a tsakanin wasu kasashen larabawa da HKI.

ABNA24 : Tun da fari, kungiyoyin na palasdinawa sun sanar da cewa za gudanar da taruka da jerin gwano da kuma jawabai a sassa daban-daban na Palasdinu domin raya ranar ta kasa da kuma nuna kin amincewa da yarjejeniyar kasashen larabawa da ‘yan sahayoniya.

A garin Khalil, Palasdinawan sun yi taro midanu shuhada’a, da Dawwar Ibn Rushdi. Sai kuma garin Tul-Karam da garin Jenin.

Garuruwan da aka yi taruka da jerin gwano sun hada Ramallah, da kuma Nablus.

Wata sanarwa ta kungiyoyin Palasdinawa ta kunshi bayyana ranar Juma’a mai zuwa a matsayin wacce za a daga bakaken tutoci domin yin tir da yarjejeniyar larabawan da yahudawa ‘yan mamaya.

342/