ABNA24 : A wani rahoto da ya fitar ofishin na OCHA, kuma ce, adadin mutanen da ambaliyar ruwa a Sudan din ta shafa ya karu daga dubu 160 a cikin kwanaki hudu zuwa kusan dubu 720 yayin.
Baya ga hakan akwai kuma gidaje dubu 71 da suka rushe, yayin da wasu karin gidajen 72,000 suka lalace, sannan sama da dabbobi 3,300 ambaliyar ruwan ta kashe.
Mutum Miliyan Guda Ambaliyar Ruwa Ta Shafa A Yankin Sahel
Sudan: Ambaliyar Ruwa Ta Rushe Dubban Gidajen Jama’a
Ofishin na OCHA ya ce, gwamnatin kasar, da hukumomin MDD, da kungiyoyi masu zaman kansu sun kai dauki da tallafin kayan abinci da na kiwon lafiya da sauransu ga mutane kimanin 200,000.
Kafin hakan dai hukumar dake kula da hasashen yanayi, ta fitar da wani gargadi na yiwuwar samun mamakon ruwan sama da ambaliyar ruwa har zuwa ranar Talata, ko da yake, tashoshin dake sanya ido kan tekun Blue Nile sun samu raguwar ruwan tekun da mataki milimita 3 a karshen makon da ya gabata.
342/