ABNA24 : Tashar talabijin ta Almayadeen ta kasar Lebanon ce ta bada wannan labarin, ta kuma kara da cewa a makon da ya gabata ne wani ba Falasdine mai suna Dawood Alkhatib ya rasu a gidan yarin Ofer Jail na HKI, saboda sakaci wajen bashi kula na likitoci da kiwon lafiya a lokacinda ya ke bukatar hakan.
Sai dai a cikin wayan Yulin da ya gabata ne wata babbar kotu a HKI ta yanke hukuncin cewa Falasdinawan da ake tsare da su a gidajen yarin HKI ba sa da hakkin a kula da lafiyarsu har’ila yau bas a da hakkin yi masu tsare-tsaren ha na yaduwar cutar korona a cikin gidajen yarin da ake tsare da su.
Kafin haka dai Falasdinawa sun koka kan cewa HKI tana sakaci wajen kola da lafiyar Falasdinawan da take tsare da su a gidajen yarin kasar, wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwar da dama daga cikinsu.
342/