10 Satumba 2020 - 09:47
​Manyan Malaman Addinin Musulunci Su 200 Sun Bada Fatawar Haramta Hulda Da Isra’ila

Manyan malaman addinin musulunci fiye da 200 ne suka bada fatawar haramcin kulla hulda da haramtacciyar kasar Isra’ila.

ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran Irna na kasar Iran ya bayyana cewa malaman sun fidda wannan fatawar ne a taron da suka gudanar ta yanar gizo a birnin Doha na kasar Qatar a ranar Lahadin da ta gabata.

Taron wanda kungiyar hadin kan malaman addinun musulunci ta shiya ya sami halattar manya-manyan malaman addini fiye da 200 daga kasashe daban-daban a duniya.

Labarin ya kara da cewa, abubuwan da suke faruwa a kasashen Larabawa a halin yanzu, na maida hulda da HKI, amincewa ne da mamayar wari mafi tsarki ga musulmi, sannan zai bawa HKI damar karasa mamayar da take yiwa Falasdinu da kuma korar sauran Falasdinawa daga kasarsu.

A ranar 13 ga watan Agustan da ya gabata ne shugaban kasar Amurka Donald Trump ya bada sanar maida huldar jakadanci tsakanin Doha da Telaviv.

342/