ABNA24 : Haniyyah ya ci gaba da cewa; “ Ko kadan kasar Hadaddiyar Daular Larabawa ba ta da wani dalili da zai sa ta kulla alaka da HKI, yarjejeniyar da ta kulla yin hidima ce kyauta ga Trump da kuma Netanyahu.”
Har ila yau Haniyyah ya bayyana takaicinsa akan yadda Saudiyya ta sauya salon mu’amala da su, sannan kuma ya yi kira gare ta da ta saki Palasdinawa da ta kame ta tsare a gidajenta na kurkuku.
Wani sashe na hirar da tashar talabijin ‘almanar’ ta yi da shi, Isma’ila Haniyyah ya yi ishara da alaka a tsakanin kungiyar Hamas da Syria, inda ya ce; Mun zauna tsawon shekaru 10 a kasar Syria, kuma mun sami kyakkyawar mu’amala daga gwamnati da al’ummar kasar.”
Haniyyah ya ci gaba da cewa; Hamas, tana yin godiya ga Syria, tana kuma yin addu’a da fatan ganin zaman lafiya ya sake dawowa cikin wannan kasa, domin bango ce da Palasdinawa su ke jingina da ita.
342/