ABNA24 : Ali Riza Mir-Yusufi ya fadawa kamfanin dillancin labaran Newsweek na kasar Amurka kan cewa dangantaka tsakanin Iran da kasar Siriya ta fi shekaru 40. Sannan Iran ta na tallafawa kasar Siriya ne da shawarwari a kan harkokin tsaro a yakin da take yi da ‘yan ta’adda kimani shekaru 10 da suka gabata.
Kafin haka dai ma’aikatar harkokin wajen kasar Amurka ta zargi kasar Iran da zama matsala a kasar Siriya, sannan ta bukaci kasar ta fidda sojojinta daga kasar Siriya, saboda ita ce matsalar kasar.
Mir-Yusufi ya kara da cewa Amurka ce matsala ga gwamnati da kuma mutanen kasar Siriya ba Iran. Don, kowa ya sani Amurka da kawayenta ne suka kakkafa kungiyoyin ‘yan ta’adda a kasar Siriya, wadanda suka hada da Jibhatun Nusra da kuma Tahrirussham da nufin kifar da kwamnatin shugaba Bashar Al-Asad.
Banda haka a halin yanzu sojojin Amurka a arewacin kasar Siriya sun hada kai da wasu yan ta’addan, suna satar danyen men fetur da ke yankin.
Sai kuma kasashen Rasha da China duk sun tabbatar cewa Amurka ta shiga kasar Siriya ne ba tare da amincewar gwamnatin kasar ba.
342/