31 Agusta 2020 - 13:35
Ana Juyayin Zagayowar Ranar Ashura A Fadin Duniya

Yau Lahadi, 10 ga watan Muharam, al'ummar musulmin Shi’a na gudanar da juyayi tare da alhinin tunawa da zagayowar ranar Ashura, ta tunawa da ranar shahadar jikan manzon Allah Muhammad (SAW) cewa da Imam Husain (A.S) da abokan tafiyarsa su 72 a garin Karbala dake kudancin Iraki a cikin shekara ta 61 bayan hijirar manzo.

ABNA24 : Saidai ranar ta bana ta zo ne a daidai lokacin da duniya ke fama da annobar cutar korona, wanda ya sanya kasashe da dama suka takaita taruwar jama’a.

A shekarun baya milyoyin ‘yan shi’a ne daga sassa daban daban na duniya ke tururruwa zuwa hubbaren Imam Husaini da ke birnin Karbala na kasar Iraki domin gudanar da juyayin wannan rana ta Ashura, amma a bana an takaita ziyarar ga mazauna kasar ne kawai saboda annobar korona.

342/