24 Agusta 2020 - 14:54
Shugaban Hukumar IAEA Zai Ziyarci Iran Ranar Litini

A wani lokaci a gobe Litini, shugaban hukumar hana yaduwar makamman nukiliya ta duniya, Rafael Mariano Grossi, zai fara wata ziyarar aiki a nan birnin Tehran na Jamhuriyar musulinci ta Iran.

ABNA24 : Idan ziyarar ta kasance it ace irinta ta farko ta Mista Grossi, tun bayan tun bayan da ya karbi shugabancin hukumar a watan Disamban bara.

An tsara yayin ziyarar tasa shugaban hukumar ta IAEA, zai gaba da manyan jami’an kasra ta Iran da dama.

Jakadan Iran kana kuma wakilin dindindin na kungiyoyin kasa da kasa a Vienna, ya ce, shugaban hukumar ta IAEA, zai ziyarci Iran ne bisa gayyata Iran da kuma huldar dake tsakanin bangarorin biyu, kuma a cewarsa yana fatan wannan ziyarar zata kara karfafa alaka tsakanin kasarsa da kuma hukumar.

Ziyarar ta Rafael Mariano, na zuwa ne kwanaki kadan bayan da kwamitin tsaro na MDD, ya yi watsi da daftarin kudirin Amurka na neman tsawaita dokar cinikin makamai ga Iran, wanda Amurka ta sha alwashin maida mummunan martani a kai ta hanyar neman a maido da illahirin takunkuman MDD kan Iran.

342/