19 Agusta 2020 - 13:19
​Al’ummomin Musulmi Da Na Larabawa Na Ci Gaba Da Yin Tir Da UAE Kan Kulla Alaka Da Isra’ila

Al’ummomin musulmi da na larabawa a kasashe daban-daban suna ci gaba da yin tir da Allawadai da matakin da gwamnatin hadaddiyar daular larabawa ta dauka, na kulla huldar diflomasiyya da gwamnatin yahudawan Isra’ila.

ABNA24 : Tashar al’alam ta bayar da rahoton cewa, Tun bayan da gwamnatin hadaddiyar daular larabawa ta bayar da sanarwar kulla alaka tsakaninta da Isra’ila a ranar Alhamis da ta gabata, Al’ummomin musulmi da na larabawa a kasashe daban-daban suna ci gaba da yin tir da Allawadai da matakin da gwamnatin ta UAE ta dauka.

A kasar Pakistan dubban musulmi sun gudanar da jerin gwanon la’antar gwamnatin UAE, tare da bayyana sarakunan kasar a matsayin maciya amanar al’ummar musulmi, musamman al’ummar Falastinu da gwamnatin yahudawan Isra’ila ke azabtar da su tsawon fiye da shekaru saba’in.

A kasashen Tunisia da Aljeriya da Libya, kungiyoyi da jam’iyyun siyasa daban-daban sun fitar da bayanai kan wannan batu, inda a jiya wasu daga cikin ‘yan majalisar dokokin Tunisia suka yi gangamin yin tir da UAE a cikin birnin Tunis.

Isra’ila ta sanar da cewa wasu daga cikin kasashen larabawa suna ta hankoron ganin sun kulla alaka da ita, amma Isra’ila ta jaddada cewa kulla alaka da gwamnatocin larabawa ba zai hana ta ci gaba da mamaye yankunan Falastinawa da take yi ba.

342/