ABNA24 : Birgediya janar Hatami wanda yake gabatar da jawabi a yau Lahadi a wani biki akan harkar tsaro, ya ci gaba da cewa; Iran din za ta yi aiki da dukkanin damar da take da ita domin samar da makaman da take bukatuwa da su, sannan kuma ta rika sayarwa da wasu kasashe da zarar an dage mata takunkumin.
Wani sashe na jawabin ministan tsaron ya kunshi cewa; Iran ta yi nasarar kerawa kanta kaso 90% da bukatun da take da su ta fuskar tsaro.
Birgadiya janar Hatami ya kuma ce; Babu wani takunkumi da zai takawa Iran birki a kokarin da take yi na kerawa kanta makaman da take bukata na tsaron kanta.
342/