17 Agusta 2020 - 10:26
Hamas: Manufar Yarjejeniyar Hadaddiyar Daular Larabawa Da Isra'ila Ita Ce Rusa Kungiyoyin Gwagwarmaya

Daya daga cikin jagororin kungiyar gwagwarmayar musulunci ta Hamas, Mahmud Zahhar, ya bayyana cewa; Yarjejeniyar da aka kulla a tsakanin Hadaddiyar Daular Larabawa da kuma HKI manufarta rusa gwagwarmaya da kawo karshen batun Palasdinu.”

ABNA24 : Mahmud Zahhar ya kuma bukaci gwamnatin kwarya-kwaryar Palasdinu da ta tsame hannunta baki daya daga yarjejeniyar Oslo da kuma janye jakadunta daga duk wata kasar larabawa wacce ta kulla alaka da ‘yan sahayoniya.

Mahmud Zahhar wanda ya jagoranci wani gangami da aka yi a bakin ginin majalisar dokoki a Gaza domin nuna kin amincewa da yarjejeniyar UAE da HKI, ya ci gaba da cewa: “ Yarjejeniyar abin kunya ce, kuma tana nuni ne da shiga sahu daya da ‘yan sahayoniya domin murkushe batun palasdinu.”

Har ila yau, Zahhar ya yi kira ga al’ummun larabawa da musulmi da su yunkura domin kalubalantar tsari da shirin mahukuntansu, sannan kuma su fito da tsarin kalubalantar makircin da ake kitsawa.

342/