ABNA24 : A wata sanarwa da shugaba Donald Trump, ya fitar, ya ce, ‘’ cikin raradi nake sanar da mutuwar dan uwa na Robert, wanda ya mutu a cikin daren nan’’
Trump ya kara da cewa ba wai dan uwa na ne kawai ba, babban amini na ne.
Dama dai an jima da aka kwantar da Robert Trump din a asibitin New York inda yake jinya, saidai ba’a bayyana ainahin ciwon dake damunsa ba.
Bayanai sun ce ba’a jima da shugaba Donald Trump, ya kai masa ziyara a asibitin na New York.
342/