ABNA24 : Majiyar muryar Iran ta nakalto Zareef yana fadar haka a ganawarsa da shugaban kasar ta Lebanon Michel Aun a safiyar yau Jumma’a.
Ministan ya kara da cewa, tare da hadin kan dukkan bangarorin siyasa na kasar, akwai fatan nutsuwa zata dawo cikin kasar. Har’ila yau Ministan ya taya shugaban kasar muryar zagayowan ranar nasarar kasar a yakin da kungiyar Hizbullah ta shiga da Isra'ila na kwanaki 33 a cikin watan Augustan shekara ta 2006.
Daga karshen ministan ya bayyana cewa kasar Iran a shirye take ta bada duk taimakon da zata iya a wannan fage.
A nashi bangaren shugaban kasar ta Lebanon Michel Aun ya yaba wa Iran kan taimakon gaggawan da ta aika zuwa kasar Lebanon bayan fashewar ranar 4 ga watan Augustan da muke ciki.
342/