13 Agusta 2020 - 13:20
Habibollah Sayyari: Sojojin Iran A Shirye Suke Domin Fuskantar Abokan Gaba

Daya daga cikin manyan kwamandojin sojan ruwan Iran Admiral Habibullah Sayyari ya bayyana cewa; Sojojin Iran suna cikin shirin ko-ta-kwana domin kalubalantar abokan gaba matukar su ka tsokani al’ummar Iran

ABNA24 : Admiral Sayyari ya bayyana hakan ne a yayin da yake kaddamar da wasu sabbin kayan aiki na aikin likitanci a jami’ar aikin likitanci ta soja, da su ka hada da asibitin tafi da gidanka da dakunan musamman na likitoci na kula da yanayin mai tsanani a filin daga.

Har ila yau, Admiral Sayyar ya ce; Baya ga ayyukan tsaro na kasa sojojin su ke yi, sojojin suna gabatar da hidimomi ga al’ummar kasa da suka hada da kare muhalli ta fuskar tsaro.

Bugu da kari Adimar Sayyari ya ce ; sojojin sun gabatar da hidima mai yawa ga ‘yan kasa domin fada da corona tun bullarta,a halin yanzu kuma sojojin suna yin ayyuka a fagen kare kai daga yaduwar cutar.

342/