ABNA24 : Yayin jawabin da ya gabatar na zagayowar ranar samun ‘yancin kasar, Shugaba Deby, ya sha alwashin ci gaba da kasancewa gimshikin samarwa da ‘yan kasarsa ‘yancin walwala.
Yaki da ta’addanci na daga cikin matakan da zamu kara karfafawa a cewar shugaba Deby cikin jawabinsa nasa.
A watan Yunin da ya gabata ne majalisar dokokin kasar Chadi ta amince da yi wa shugaban kasar mai shekaru 68 karin girma zuwa mukamin marshal mukami mafi girma a aikin soji.
Idriss Deby dai ya shafe shekaru 30 yana shugabancin wannan kasa ta Chadi.
Kuma Majalisar dokokin kasar ta ba shi wannan mukamin ne na marshal bayan wani farmaki da ya jagoranta kan yaki da kungiyar boko haram a watan Afrilu, a matsayin maida martani kan wani karamin harin kunfiyar da ya yi sanadin mutuwar sojojin Chadi kimanin 100.
342/