ABNA24 : Ya zuwa jiyan an tabbatar da mutuwar mutane 81 a fadan da aka yi amfani da manyan bindigogi, kamar yadda kakakin sojan kasar ya sanar.
Kakakin sojan kasar Ruai Koang ya shaidawa kamfanin dillancin labarun Reuters cewa; Matasan da suke dauke da makamai a yankin Greater Tonj ne su ka fara kai farmaki akan sojojin.
Koang ya kara da cewa; Sojoji 55 ne su ka rasa rayukansu sai kuma fararen hula 26.
An sake samun dawowar zaman lafiya a cikin yankin da lamarin ya faru kamar yadda kakakin sojan ya fada.
342/