9 Agusta 2020 - 14:29
An Bude Asibitin Iran Na Wucin Gadi A birnin Beirut Na Kasar Lebanon

An bude asbitin Iran na wucin gadi ko asbitin tafi da gidanka a birnin Beirut babban birnin kasar Lebanon.

ABNA24 : Majiyar muryar Jumhuriyar Mususlunci ta Iran ta bayyana cewa an bude asbitin ne da nufin jinyar wadanda suka ji rauni sanadiyyar hatsarin da ya auku a tashar jiragen ruwa na birnin a ranar Talatan da ta gabata, wanda ya kai ga raunata mutane kimani 6000 sannan wasu fiye da 150 suka rasa rayukansu.

Muhammad Jawad Firuzniyo, jakadan JMI a birnin Beirut ya bayyana cewa Tehran a shirye take ta taimakawa kasar Lebanon bayan fashe-fashen da suka auku a makon da ya gabata, da kuma sake ginin wuraren da suka lalace.

Hakama shugaban hukumar bada agajin gaggawa na kasar Iran ko Hilala Ahmar, Farid Muradiyon ya bayyana cewa asbitin da hukumarsa ta bude yana da bangaren ICU wato kula na musamman, sannan akwai wuraren ayyukan tiyata da kuma sauran sassa.

342/