ABNA: Tahsin Khaffaji kakakin gamayyar jami’an tsaron ya fadawa kamfanin dillancin labaran “Waa” na kasar ta Iraqi kan cewa, ragowar mayakan kungiyar Daesh su na shirin kaddamar da hare-hare a kasar a dai-dai lokacinda kasar ta ke fama da tsananin ra na da kuma yaduwar annobar cutar Korona.
Khaffaji ya kara da cewa a halin yanzu jami’an tsaron kasar sun samar da maduban hangen nesa na musamman don ayyukan rani, wadanda zasu taimaka wajen gano kai kawon ‘yan ta’adda a duk fadin kasar. Ya kuma kara da cewa za su yi amfani da jiragen leken asiri don karfafa ayyukan tsaro a duk fadin kasar.
Tun cikin watan Nuwamban shekara ta 2017 ne dai, aka kawo karshen ikon kungiyar ‘yan ta’adda ta Daesh a kasar Iraqi, amma har yanzun akwai daddaikunsu a boye a wurare da dama a kasar.
342/