28 Yuli 2020 - 11:40
Kungiyar Tattalin Arziki Ta Yammacin Afirka ( ECOWAS) Ta Bukaci “Yan Majalisar Kasar Mali Su Bar Aiki, Sannan Kuma A Kafa Gwamnatin Hadin Kan Kasa

A jiya Litinin ne shugaban kasar Najeriya Muhamamdu Buhari tare da wasu shugabannin kasashen yammacin Afrika su ka bukacin ‘yan majalisar dokokin kasar Mali 31 da su yi murabus daga aikinsu, saboda a warware rikicin da kasar take fama da shi.

ABNA24: Shugabannin kasashen yammacin Afirkan sun bayyana cewa murabus din ‘yan majalisar daya ne daga cikin hanyoyin kawo karshen dambaruwar siyasar da kasar ta Mali take ciki.

An dauki wannan matakin ne dai a yayin taro ta hanyar bidiyo da shugabannin gwamnatocin kasashen kungiyar ta ECOWAS su ka yi akan rikicin kasar Mali.

Karamin ministan harkokin waje na Najeriya Ambassador Zubairu Dada ne ya karanta abubuwan da aka cimmawa daga fadar Villa da ke Abuja, inda shugaba Muhamamdu Buhari ya shiga tattaunawar ta bidiyo.

342/