27 Yuli 2020 - 11:28
An kashe Mutane 120 A Wani Sabon Rikicin Kabilanci A Yankin Darfur Na Sudan

Rahotannin da suke fitowa daga kasar Sudan sun bayyana cewa an sami mutuwar mutane 120 a wani sabon fada da ya barke a kauyen Mistari da ke jahar Darfur ta yamma.

ABNA24: Bugu da kari an yi kone-konen gidajen a kauyen da shagunan kasuwanci.

Wannan dai shi ne fada karo na biyu na kabilanci a cikin yankin na Darfur a kwanaki kadan.

Fira ministan kasar Sudan Abdullah Hamduk ya sanar da cewa; Daga nan zuwa Alhamis za a aike da jami’an tsaro zuwa yankin domin tabbatar da tsaro ga mutane da bayar da kariya ga gonaki.

Yankin Darfur ya fuskanci matsanancin rikici a 2003 inda aka yi kiyasin kashe mutanen da su ka haura 300,000, da kuma wasu miliyan biyu da rabi da aka raba da matsugunansu.

342/