ABNA24: Bugu da kari tattaunawar bangarorin biyu ta tabo yadda za a bunkasa harkokin kasuwanci da kuma batutuwa masu yawa da su ka shafi duniyar musulmi.
Ministocin biyu su kuma amince da yin taron kwamitin hadin gwiwa na kasashen biyu saboda bunkasa harkokin kasuwanci.
Bugu da kari, ministan harkokin wajen Iran ya bukaci takwaransa na Malaysia da kasarsa ta ke memba a cikin kungiyar kasashen musulmi da ta taka rawa domin kawo karshen yakin Yemen ta hanyoyin siyasa.
Muhammad Jawad Zarif ya tabbatar da cewa Iran za ta bayar da goyon baya akan duk wani kokari da Malaysia za ta yi domin ganin an sami zaman lafiya mai dorewa a kasar Yemen da kawo karshen yaki.
Har ila yau Zarif ya jinjinawa Malaysia akan yadda take bayar da goyon baya ga al’ummar Palasdinu.
A nashi gefen, Dato Hishamuddin Husain ya tabbatar da matsayar kasarsa na ci gaba da goyon bayan al’ummar Palasdinu.
342/