16 Yuli 2020 - 13:56
Muhsin Riza’i: Yakin Da Ake Yi Da Iran A Yanzu, Ya Fi Na Lokacin Saddam Muni

Sakataren Majalisar Fayyace Maslahar tsarin musuluci ta Iran , Muhsin Riza’i ya bayyana cewa; Yakin da ake yi da Iran a yanzu ya fi tsanani da muni akan wanda aka kallafawa Iran din ta hanyar Saddam a karnin da ya wuce.

ABNA24: Muhsin Riza’i, wanda ya gabatar da jawabi ajiya Labara, ya ce; Yakin na yanzu, yana da muni mai tsanani akan wanda aka kallafawa Iran a tsakanin 1980-1988, domin a wancan lokacin abokin gaba yana amfani da makamai masu guba, amma yanzu abokin gaba yana amfani da wata hanya da ta fi wancan mufi, saboda Amurka ba ta kasa a gwiwa wajen keta hakkin bil’adama da kuma keta yarjeniyoyi na kasa da kasa.

Muhsin Riza’i, ya kara da cewa; banbancin wancan yakin da wannan shi ne, a wancan yakin ba dukkanin mutane ne su ke jin karar bama-bama ba da ake jefawa ba, kuma Saddam daidai da Trump ya yi watsi da kudurorin Majalisar Dinkin Duniya.

Sakataren majalisar fayyace maslahar tsarin musuluncin ya ci gaba da cewa; Da ace ba mu takawa Saddam birki ba a wancan lokacin to da Majalisar Dinkin Duniya ta goyi bayansa, a yau kuwa Trump ya keta yarjejeniyar Nukiliya kuma kasashen turai sun keta alkawalinsu suna biye wa Amurka a kokarin sake tsawaita takunkukumin saye da sayar da makamai akan Iran.

Har ila yau Riza’i ya jaddada wajabci ci gaba da hadin kai tsakanin dukkanin bangarorin gwamnati da al’umma domin samun galaba akan mawuyacin halin da ake ciki.

342/