14 Yuli 2020 - 14:05
Shugaba Hassan Rauhani Ya Ce: Iran Za Ta Yi Nasara A Yakin Tattalin Arzikin Da Amurka Ta Shelanta A Kanta

Shugaban na kasar Iran ya kira yi dukkanin bangarorin gwamnati da su yi aiki cikin hadin kai da juna, musamman a wannan lokaci da ake fuskantar tsanani na tattalin arziki saboda takunkumi da kuma cutar corona.

(ABNA24.com) Shugaban na kasar Iran ya ci gaba da cewa; Tabbas Iran tana gab da samun nasara a yakin na tattalin arziki da Amurka ta shelanta a kanta.

Shugaban na kasar Iran dai ya bayyana hakan ne a yayin taron majalisar koli ta tattalin arzikin kasa wacce ta kunshi banagrori uku na gwamnati da aka kafa bisa umarnin jagoran juyi Imam Khamnei domin magance matsalolin tattalin arziki.

An kafa majalisar ne dai bayan ficewar Amurka daga yarjejeniyar Nukilya da kuma kakaba wa Iran takunkumai.

342/