13 Yuli 2020 - 11:43
Farashin Danyen Man Fetur Ya Fadi A Kasuwar Duniya

A daidai lokacin da cutar corona take ci gaba da daukar rayukan mutane a Amurka, farashin danyen man fetur ya sake faduwa a yau Litinin.

(ABNA24.com) Tashar talabijin din CBS ta Amurka ba bayar da labarin cewa; Da safiyar yau Litinin kowace gangar danyen mai na Taxes an sayar da ita akan dalar Amurka 40,08

A jiya Lahadi an sami Karin mutanen da su ka kai dubu 60 masu dauke da cutar ta corona, wanda shi ne mafi girma tun bullar cutar a kasar Sin.

Manyan ‘yan kasuwa masu manyan kamfanoni a cikin kasar ta Amurka suna son a bude harkokin kasuwanci, yayin da jami’an kiwon lafiya su ke gargadi akan hakan.

342/