4 Yuli 2020 - 11:34
​An Dakatar Da Shugabannin Asusun Inshorar Kyautata Rayuwa Ta NSITF A Najeriya

Ma’aikatar Kwadago ta ce Shugaba Buhari ya amince da dakatar da Manajan Daraktan Asusun Inshorar Kyautata Rayuwa (NSITF), Adebayo Somefun da sauran Manyan Daraktocin hukumar nan take.

(ABNA24.com)  Rahotanni sun ce Adebayo da Manyan Daraktocin da kuma Manyan Manajojin Gudanarwa da Mataimakansu sun tafi hutun dole nan take.

Kakakin Ma’aikatar Kwadago Charles Akpan, cikin wata sanarwa ya ce, “Dakatarwar ta biyo bayan hujjojin da ke nuna shugabannin na Asusun Inshorar Kyautata Rayuwa NSITF sun karya dokokin kashe kudaden gwamnati, baya ga kuma aikata wasu laifuka na daban”.

Wadanda aka dakatar din za su gurfana a gaban kwamitin hadin gwiwa mai bincikar karya dokar kashe kudade da sauran laifuka a hukumar daga shekarar 2016 zuwa yanzu.

Sanarwar ta umarci dukkanin wadanda aka dakatar da su mika kayan gwamnatin da ke hannunsu ga sauran jami’ai wadanda suka fi girman matsayi a sassan da suka bari.

Minista Chris Ngige ya nada jami’an da za su rike mukaman wadanda aka dakatar din daga ranar Litinin 6 ga watan Yuli, yayin da Shugaban Kwamitin Amintattu, Austin Enajemo Isire zai ja ragamar hukumar.

342/