29 Yuni 2020 - 07:03
​Rasha Da Syria: Amurka Na Amfani Da Batun 'Yan Gudun Hijira Domin Taimakawa 'Yan Ta’adda

Kasashen Rasha da Syria sun yi gargadin cewa Amurka tana kokarin taimakawa kawayenta ‘yan ta’adda ta hanyar amfani da sansanin ‘yan gudun hijira na Rukban da yake kusa da iyaka da kasar Jordan.

(ABNA24.com)  Kasashen Rasha da Syria sun yi gargadin cewa Amurka tana kokarin taimakawa kawayenta ‘yan ta’adda ta hanyar amfani da sansanin ‘yan gudun hijira na Rukban da yake kusa da iyaka da kasar Jordan.

Bayanin ya ci gaba da cewa; A wani karon Amurka ta sake yin halinta, inda ta bayyana cewa a shirye ta ke ta fitar da dukkanin ‘yan gudun hijirar da suke cikin sansanin Rukban saboda kawai ta taimakawa ‘yan ta’adda.”

Bayanin na kasashen biyu ya kuma kara da cewa: Amurka tana son bayar da taimakon soja ta kawayenta da dukkanin kayan aiki, wanda ya sabawa ka’idojin kungiyoyin kasa da kasa na bayar da agaji.”

A watan da wuce ma dai kungiyar “Amnesty International “ ta kira yi gwamnatin Jordan da ta bayar da taimakon aikin likitanci na gaggawa ga sansanin ‘yan gudun hijirar domin fada da cutar corona.

Kungiyar ta Amnesty ta yi gargadin cewa; rashin kula da sansanin ‘yan gudun hijirar na Rukbana da ke kan iyakar Syria da Jordan, yana jefa rayuwar dubban mutanen da suke cikinsa a cikin hatsari bayan bullar cutar corona.



/129