(ABNA24.com) Ministan ya kara da cewa zasu zabi kayaki kimani 200 sannan a sanya masu farashi wanda mutane zasu iya saya. Idan kuma an same shi da farshi wanda ya sabawa na gwamnati to za’a dauki matakan latabatarwa ga wadanda suke yi hakan.
Rawul ya bayyana cewa shirin zai fara aiki daga mako mai zuwa kuma zai shafi kashi 70 zuwa 80 % na bukatun mutane na yau da kullum .
A cikin watannin da suka gabata kudden kasar Lebanon “lirah” ya rasa darajarsa sosai idan an kwatanta da dalar Amurka, sabo da lalacewar tattalin arzikin kasar da kuma takunkuman tattalin arziki wadanda gwamnatin kasar Amurka ta dorawa kasar Siriya makobciyarta.
/129
Lebanon: Ministan Tattalin Arziki Da Kasuwanci Ya Ce Gwamnati Zata Fara Shirin Tallafawa Talaka Da Kayan Masarufi Mai Sauki
28 Yuni 2020 - 07:35
Lambar labari: 1050905
Ministan tattalin arziki da kasuwanci na kasar Lebanon Rawul Ni’imah ya bayyana cewa gwamnatin kasar zata fara wani shiri don tallafawa masu karamin karfi a kasar masarufi mai saukin farashi don rage radadin da suke fama da shi saboda fadwar darajar kudaden kasar.