(ABNA24.com) Tashar RT ta bayar da rahoton cewa, a cikin rahoton da hukumar lafiya ta duniya ta fitar ta sanar da cewa, ya zuwa yanzu mutane 230,454 ne aka tabbatar da sun harbu da cutar corona a fadin nahiyar Afirka, yayin da 6,218 daga cikinsu suka rasa rayuwansu, wasu kimanin 106,000 kuma suka warke.
Bayanin hukumar WHO ya ce, har yanzu kasar Afirka ta kudu ce a kan gaba, inda yawan mutanen da suka kamu ya kai 65,736 a kasar, sai kuma Masar 41,303, yayin da Najeriya take biye mata da mutane 15,181.
A bangaren wadanda suka rasa rayukansu a nahiyar Afirka sakamakon kamuwa da cutar corona kuwa, kasar Afirka ta kudu dai ita ce kan gaba da mutane 1,423, sai kuma kasara Masar tana biye mata 1,422, yayin da Aljeriya take da mutane 760.
Kafin wannan lokacin dai hukumar lafiya ta duniya ta yi gargadin cewa, idan ba a dauki matakan da suka dace ba, mai yiwuwa cutar corona ta yi babbar illa ga kasashen nahiyar Afirka, kamar yadda kuma za ta iya haifar da matsaloli na yunwa a wasu kasashen nahiyar, sakamakon yadda ta durkusar da tattalin arzikinsu.
/129
16 Yuni 2020 - 09:16
Lambar labari: 1047206
Hukumar lafiya ta duniya ta bayar da bayanin cewa, adadin mutanen da suka kamu da corona a nahiyar Afirka ya zuwa yanzu ya haura mutane dubu 230.