Ehlibeyt (as) Haber Ajansı ABNA - Sojojin haya wadanda suke aikiwa gwamnatocin Saudiya da kawayenta a yakin da suka dorawa kasar Yemen, a jiya Lahadi sun kai hare-hare a wurare daban daban a lardin Hudaida, inda mutane 4 suka yi shahada, sannan wasu 18 suka ji rauni.
Majiyar muryar Jumhuriyar Musulunci ta Iran ta nakalto majiyar gwamnatin kasar ta Yemen tana cewa sojojin hayar sun kai farmaki cikin daren Lahadi a kan unguwara Azzahoor inda suka kashe mutane 4, sannan wasu 18 kuma suka ji rauni kuma suke jinya a asbitocin lardin na Hudaida, duk tare da karancin kayan aiki da suke fama da shi.
Banda haka labarin ya kara da cewa jiragen yakin kawancen Saudiyyan sun kai hare-hare har sau 18 kan garin Sarwah, sannan wasu 3 yankin Sa’adah da kuma wasu biyu a yankin Hijja. Dukkansu a jiya Lahadi.
/129
1 Yuni 2020 - 07:35
Lambar labari: 1042214
Sojojin haya wadanda suke aikiwa gwamnatocin Saudiya da kawayenta a yakin da suka dorawa kasar Yemen, a jiya Lahadi sun kai hare-hare a wurare daban daban a lardin Hudaida, inda mutane 4 suka yi shahada, sannan wasu 18 suka ji rauni.