30 Mayu 2020 - 09:06
Iraqi:Dakarun Hashdushaabi Sun Kakkabo Jirgin Leken Asiri Na Daesh

Majiyar dakarun Hashdushaabi na kasar Iraqi ta bayyana cewa dakarun rundunar sun sami nasarar kakkabo wani jirgin liken asiri na kungiyar Daesh a lardin Diyala a jiya Jumma’a.

(ABNA24.com) Majiyar dakarun Hashdushaabi na kasar Iraqi ta bayyana cewa dakarun rundunar sun sami nasarar kakkabo wani jirgin liken asiri na kungiyar Daesh a lardin Diyala a jiya Jumma’a.

Tashar talabijin ta Al-alam a nan Tehran ta nakalto wani bayani wanda dakarun suka fitar a jiya jumma’a na cewa rundunar dakarun ta 23 da kuma ta 24 ne suka gudanar da wani sumame a yankin diyala a arewa maso gabacin garin Bakuba inda suka gano wata mabuyar ‘yan kungiyar ta Daesh suka wargazata, sannan suka kakkabo jirgin liken asirin kungiyar a yankin.

Gwamnatin Amurka wacce ta kafa kungiyar yanta’adda ta Daesh tana son sake dawo da kungiyar a kasar Iraqi bayan da ta tabbatar da cewa za’a tilasta mata ficewar daga kasar sanadiyyar kissan da tayi wa shahid Kasim Sulaimani da kuma shahid Mahdi Muhandis a farkon wanna shekara.



/129