(ABNA24.com) Shugaban hukumar lafiya ta duniya WHO Tedros Adhnom Gebreyesus, ya ce ana samu gagarumin ci gaba, a kokarin da ake na yaki da annobar corona a nahiyar Afirka.
Gidan radiyon Faransa ya bayar da rahoton cewa, a lokacin da yake gabatar da taron manema labarai a game da matsayin wannan cuta a duniya, Tedros ya ce yanzu haka hukumar WHO na shirin tura karin kayayyakin gwaje-gwaje zuwa nahiyar ta Afirka.
Shugaban hukumar ta WHO ya ce a halin da ake ciki kasashen Afirka sun samar da dakunan gwajin cutar corona kimanin 51, sabanin karancin wuraren gwajin da nahiyar ta fuskanta a makwannin da suka gabata.
A cikin wannan wata na Mayu, Hukumar Lafiya ta Duniya tayi hasashen cewar akalla mutane miliyan 200 annobar coronavirus za ta kama a nahiyar Afirka a cikin shekara guda, yayin da 150,000 za su iya mutuwa, matukar dai hukumomi suka gaza daukar matakan da suka dace wajen dakile annobar.
/129
28 Mayu 2020 - 05:07
Lambar labari: 1040862
Shugaban hukumar lafiya ta duniya WHO Tedros Adhnom Gebreyesus, ya ce ana samu gagarumin ci gaba, a kokarin da ake na yaki da annobar corona a nahiyar Afirka.