(ABNA24.com) Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Human rights Watch ta fitar da rahoton cewa karuwar kai hare haren kungiyoyin da ke rajin jihadi a kasar Burkina Faso tun a shekara ta 2017 ya sanya rufe makarantu sama da 2000 a kasar, ita ma maikatar ilimi ta kasar ta bayyana cewa rufe makaratnu 2500 ya sanya sama da dalibai 350,000 rashin samun ilimi.
Har ila yau rahoton ya ci gaba da cewa sama da malamai da ma’aikatan ilimi 222 ne aka ritsa da su a hare haren na yan ta’adda, ya kara da cewa yan ta’adda sun kai hare hare 126, kana kuma suna barazana ga malam makaranta da dalibai.
Daga lokacin fara kai hare hare kan makarantu zuwan yanzu kimanin profesoshi 12 ne aka kashe wasu 17 kuma an yin garkuwa da su, Sai dai an sake rufe makarantu da jami’oi a kasar saboda bullar cutar Korona a tsakiyar watan maris sai dai ana sa ran sake bude makarantun a ranar 1 ga watan Yuli kamar yadda gamnatin kasar ta ce.
/129
27 Mayu 2020 - 04:15
Lambar labari: 1040384
Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Human rights Watch ta fitar da rahoton cewa karuwar kai hare haren kungiyoyin da ke rajin jihadi a kasar Burkina Faso tun a shekara ta 2017 ya sanya rufe makarantu sama da 2000 a kasar, ita ma maikatar ilimi ta kasar ta bayyana cewa rufe makaratnu 2500 ya sanya sama da dalibai 350,000 rashin samun ilimi.