(ABNA24.com) Shugaban ƙasar Iran Dakta Hasan Rouhani ya bayyana cewar wajibi ne dukkanin himma da ƙoƙarin jami’an gwamnati su zamanto wajen kyautata yanayin tattalin arziƙin ƙasa, kyautata rayuwar al’umma da kuma karfafa makomar ƙasa.
Shugaba Rouhani ya bayyana hakan ne a yayin taron kwamitin tattalin arziki na ƙasar Iran da aka gudanar ƙarƙashin jagorancinsa don tattauna hanyoyin da za a bi wajen samar da kayayyakin buƙatun yau da kullum na al’umma a ƙoƙarin da ake yi na kyautata rayuwar al’umma musamman a irin wannan yanayi da ake ciki a duk faɗin duniya inda ya jaddada muhimmancin samar da abubuwan da mutane suke buƙata wajen gudanar da rayuwarsu ta yau da kullum.
A yayin taron Ministan harkokin wajen, Dakta Muhammad Jawad Zarif yayi ƙarin haske kan irin ayyukan da ma’aikatarsa ta yi a fagen diplomasiyya wajen ƙarfafa tattalin arzikin Iran da kuma kyautata alaƙa da sauran ƙasashen duniya.
Shi ma a nasar ɓangaren, gwamnan babban bankin ƙasar ta Iran. Abdolnaser Hemmati yayi ƙarin bayani kan yadda bankin ya samar da kuɗaɗen waje musamman ga masana’antu don samar da abubuwan da ake buƙata a cikin gida a fagen ƙere-ƙere da samar da kayayyakin da ake buƙata.
/129
16 Mayu 2020 - 06:26
Lambar labari: 1037242
Shugaban ƙasar Iran Dakta Hasan Rouhani ya bayyana cewar wajibi ne dukkanin himma da ƙoƙarin jami’an gwamnati su zamanto wajen kyautata yanayin tattalin arziƙin ƙasa, kyautata rayuwar al’umma da kuma karfafa makomar ƙasa.