9 Mayu 2020 - 05:44
Iran : Yawan Masu Kamuwa Da Covid-19, Ya Ragu Matuka

A Iran, mutane 55 ne aka sanar sun rasa rayukansu sakamakon kamuwa da cutar coronavirus a cikin sa’o’i 24 da suka gabata, wanda ya sanya adadin mutanen da cutar ta kashe a fadin kasar ya kai 6,541.

(ABNA24.com) A Iran, mutane 55 ne aka sanar sun rasa rayukansu sakamakon kamuwa da cutar coronavirus a cikin sa’o’i 24 da suka gabata, wanda ya sanya adadin mutanen da cutar ta kashe a fadin kasar ya kai 6,541.

Alkalumman wandanda suka harbu da cutar kuwa a cikin sa’o’in 24 shi ne 1,556 wanda ya sanya adadin wanda suka harbu da cutar a fadin kasar ya kai 104, 691 kamar yadda ministan lafiya na kasar ya sanar.

Wannan adadin a cewar, Kianoush Jahanpour, shi ne mafi kankanci da aka taba samu a cikin yini guda a kasar tun bayan bullar cutar.

Adadin kuma wadanda suka warke daga cutar ya kai 83,837 saidai har yanzu akwai wasu mutum 2,711 wadanda ke cikin mawuyacin hali a cewar jami’in.



/129