(ABNA24.com) Kungiyar ‘yan jarida ta kasa a Najeriya NUJ, ta yi kira ga hukumomi a kasar da su dauki matakan da suka dace wajen tabbatar da an bai wa ‘yan jarida kariya, tare da bunkasa ‘yancin kafafen watsa labarai.
Wannan kira NUJ ya zo ne a yau Lahadi ranar ‘yan jarida ta duniya, a daidai lokacin da ake tunawa da wannan rana a ko’ina cikin fadin duniya.
An dai ware ranar 3 ga watan Mayu ne a matsayin ranar ‘yan jarida ta duniya a wani mataki na tattaunawa a kan ‘yancin kafafen watsa labarai da kuma matakan ci gaba da ba su kariya.
Sannan ana amfani da wannan lokacin wajen tuna gwarazan ‘yan jarida wadanda suka rasa rayukansu a yayin ayyukansu a duniya.
Taken taron na bana shi ne; “Aikin Jarida ba tare da tsoro ko alfarma ba.”
NUJ na ganin taken na bana a matsayin nazari mai kyau musamman a daidai lokacin da corona ta addabi duniya, wanda hakan ya zama sabon kalubale ga ‘yan jarida musamman masu kawo rahotanni kan wannan cuta.
/129
4 Mayu 2020 - 03:41
Lambar labari: 1033096
Kungiyar ‘yan jarida ta kasa a Najeriya NUJ, ta yi kira ga hukumomi a kasar da su dauki matakan da suka dace wajen tabbatar da an bai wa ‘yan jarida kariya, tare da bunkasa ‘yancin kafafen watsa labarai.