(ABNA24.com) Kasashen Jamus, Faransa da Italiya da kuma babban wakilin kungiyar tarayyar turai sun yi kiran da a tsagaita wutar jin kai a Libiya a wannan lokaci na watan Ramadana.
A wata sanarwar bai daya da suka fitar da yammcin jiya, bangarorin sun ce, sun goyi bayan babban sakataren MDD, , Antonio Guterres, da kuma wakiliyarsa ta musamman ta wucin gadi kan rikicin Libiya, Stéphanie Williams, na neman tsagaita wutar jin kai a kasar ta Libiya.
Rikicin a cewar bangarorin na ci gaba da kazanta a baya bayan nan, wanda kuma babban abun damuwa ne musamman ga al’ummar kasar ta Libiya wanda suka jima a cikin halin ni ‘yasu.
A don haka ne mu ke kira ga masu rikici a kasar dasu dubi alfarmar wannan wata na Ramadana da kum ahalin da duniya ke ciki game da cutar corona su koma kan teburin tattaunawa game da shirin tsagaita wuta mai daurewa, inji sanarwar kasashen kasashen turan.
Kasar Libiya ta kasa samun gindin zama ne tun bayan kifar da mulkin tsohon hsugaban kasar mirigayi Mua’ammar Ghaddafi a cikin shekara 2011, inda yanzu haka kasar ke fama da gwamnatoci guda biyu, da suka hada da ta Fayez Al-Sarraj ta Tripoli dake samun goyan MDD, sai kuma ta Khalifa Haftar dake rike da ikon gabashin kasar.
/129
26 Afirilu 2020 - 06:15
Lambar labari: 1029858
Kasashen Jamus, Faransa da Italiya da kuma babban wakilin kungiyar tarayyar turai sun yi kiran da a tsagaita wutar jin kai a Libiya a wannan lokaci na watan Ramadana.