(ABNA24.com) Har ila yau shugabannin kasashen biyu sun tattauna matsalar annobar corona da ta addabi duniya, tare da nuna fatan ganin an kawo karshenta cikin kankanen lokaci mai zuwa.
Shugaban na kasar Iran ya kuma yi kira da a yi aiki tare a tsakanin kasashen biyu domin fuskantar wannan matsala ta hanyar musayar kwarewar da su ke da ita.
A nashi gefen, shugaban kasar Rasha ya bayyana fatansa na ganin an aiwatar da dukkanin yarjejeniyar da aka kulla a tsakanin kasashen biyu, tare da jaddada karfin alakar Moscow da Tehran.
Dangane da takunkumin da Amurka ta kakaba wa Iran kuwa, shugaban na kasar Rasha Vladimir Putin ya ce hakan yana cin karo da kare hakkin dan’adam, tare da yin suka akan yadda yammacin turai su ke yin fuska biyu akan batun kare hakkin dan’adam
/129
Shugaban Kasar Rasha Ya Tattauna Ta Wayar Tarho Da Takwaransa Na Iran Akan Bunkasa Alakar Kasashen Biyu
22 Afirilu 2020 - 05:29
Lambar labari: 1028481
A yayin tattaunawar, shugaban kasar Iran Dr. Hassan Rauhani ya bayyana muhimmancin yin aiki tare a tsakanin Tehran da Moscow, da kuma bunkasa alakar tasu ta fuskoki daban-daban.